An kama mutane 11 a jihar Jigawa da suka yiwa yarinya ‘yar shekara 12 fyade

0
1792

Jami’an ‘yan sanda sun cafke mutane 11 da laifin yiwa wata karamar yarinya ‘yar shekara 12 fyade.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri shine ya bayyana haka ga jaridar Daily Post a Dutse.

Ya ce lamarin ya faru a unguwar Limawa dake cikin garin Dutse babban birnin jihar ta Jigawa.

Jinjiri ya bayyana cewa sun kama mutanen ne bayan wani rahoto da suka samu cewa wani Alhaji Zuwai mai shekaru 57 dake kauyen Ma’ai dake cikin karamar hukumar ta Dutse, an ganshi a cikin kasuwa yana kokarin yaudaro wata yarinya ‘yar shekara 12 zuwa wani boyayyen wuri domin yayi lalata da ita.

Ya ce ‘yan sandan sun samu nasarar kama mutumin, kuma a yayin hira da yarinyar ta lissafo mutane 11 da suke lalata da ita a wurare daban-daban.

Kakakin rundunar ya ce tuni an cafke mutane 11 din kuma duk sun amsa laifin su na yi mata fyade.

Ya kara da cewa har yanzu ana cigaba da bincike akan lamarin a ofishin CID dake Dutse.

A wani rahoto makamancin haka kuma Press Lives ta kawo muku rahoton yadda aka kama wani mai unguwa da ya yiwa wata budurwa cikin shege a lokacin da ake shirin daura mata aure.

Asirin mai unguwar dai ya tonu ne a lokacin da ake shirin daurin auren budurwar, inda aka gano cewa tana dauke da cikin wata uku da wannan mai unguwa a jihar Adamawa.

Sai dai mai unguwar ya bukaci a bashi auren yarinyar zai cigaba da daukar nauyinta, inda su kuma iyayen yarinyar suka nuna hakan ba zai yiwu ba.

Ga dai labarin dalla-dalla a kasa: Asirin mai unguwa ya tonu bayan an gano ya yiwa budurwa cikin shege a lokacin da ake shirin daura mata aure

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here