An kama kyakkyawar budurwa da laifin damfara a yanar gizo a Najeriya

0
529

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya reshen jihar Legas, ta kama wasu ‘yan damfara guda biyar, ciki hadda wata kyakkyawar budurwa mai amfani da kafar sadarwa ta Instagram, Adedamola Adewale.

‘Yan damfarar guda biyar an kama su a wurare daban-daban a jihar ta Legas a lokacin wani sumame da jami’an suka kai maboyar su.

Adewale mai shekaru 20, da abokanan harkarta, Lamina Hamzat Ajibola, an kama su a a yankin Agungi dake Lekki, jihar Legas, inda Israel Onyebuchi, Emmanuel Olayode da Valentine Nwokorie aka kama su a Ibeju Lekki duka a jihar ta Legas.

Adedamola Adewale da abokin harkarta | Hoto Linda Ikeji Blog

A cewar hukumar, sun samu nasarar kama budurwar da abokintan ne bayan sun samu wasu rahotanni dake alakanta su da damfara a yanar gizo, an kama su a wani katon gida na wasu yaya da kani Lasisi Wasiu Adeleke da Lasisi Rilwan Adeniyi, wadanda suka gudu ake nemansu.

A lokacin da aka gabatar da bincike a kanta, Adewale wacce aka fi sani da Adeherself, ta amsa laifinta, inda ta ce dama tana dan taba wannan harka a yanar gizo.

An samu abubuwa a wajen wadanda ake zargin da suka hada da mota mai kirar Toyota Camry, da kuma kudi kimanin naira miliyan tara, wadanda aka samu a cikin asusunta.

Su kuma sauran masu laifin, Onyebuchi, Olayode da Nwokorie an kama su da hannu wajen damfara. Suma an kama su bayan wani sumame da jami’an suka kai.

Onyebuchi, Olayode, da Nwokorie | Hoto Linda Ikeji Blog

Rahotanni sun nuna cewa Nwokorie yana damfarar mutane ne ta hanyar aika musu da hotunan matan Turawa tsirara yana damfararsu kudi, inda shi kuma Onyebuchi aka kama shi da laifin damfarar wata mata da soyayyar karya.

Abubuwan da aka samu daga wajen masu laifin suna hada da na’ura mai kwakwalwa ta tafida gidanka da kuma wayoyi. Duka dai za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kansu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here