An kama fasto da ya yiwa yara maza guda 14 fyade ta hanyar yin luwadi da su

0
232

An kama wani mutumi mai shekaru 30 a duniya a jamhuriyyar dimokuradiyyar Congo, da laifin yiwa yara guda 14 fyade ta hanyar yin luwadi da su ya gudu ya bar su cikin mawuyacin hali.

Asibitin Panzi Foundation dake birnin Bukavu sune suka bayyana wannan labari ga kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Talata 12 ga watan Mayu, inda asibitin ya bayyana cewa an kawo yaran asibitin a watan da ya wuce bayan an kama faston.

An kama mutumin a watan Afrilun shekarar nan ta 2020, cewar Julien Namegabe ta sanar da AFP.

Duka yaran sun fito daga gidaje daban-daban, inda suke tsakanin shekaru 8 zuwa 15.

Mutumin yayi amfani da kyaututtuka ya rufe bakin yaran ne tsawon makonni masu yawa, a cewar asibitin na Panzi.

Wani ma’aikacin lafiya mai suna Evariste Kajibwami, wanda ya dinga kula da yaran tun bayan lokacin da aka kwantar da su a asibiti, ya ce yaran duka suna cikin damuwa, tsoro da kuma kunya.

Asibitin dai ya ce zai cigaba da taimakawa yaran har sai an bi musu hakkinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here