An kama dan gidan Liman da ya kashe abokin shi akan wayar salula

0
1052

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama Abdulrahman Olayiwola, dan gidan babban Limamin unguwar Isale Oja dake Agege, da laifin kashe abokin shi da aka bayyana sunanshi da Pelumi, bayan rikici ya hado su akan wayar salula da aka sace.

A cewar ‘yan sandan, Pelumi ya bawa Abdulrahman wata waya da ya sato ya ajiye mishi. Sai rikici ya barke tsakaninsu a lokacin da Abdulrahman yaki ya mayarwa da Pelumi wayar a lokacin da ya bukace ta. Sai da budurwar Pelumi da ‘yar uwar Abdulrahman suka sanya baki sannan ya bayar da wayar.

Sai dai kuma, washe gari rikicin ya kara barkewa, inda suna cikin fadan sai Abdulrahman ya dauki wata kwalba ya cakawa abokin nashi a wuya, hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi.

Daga baya an sanar da ‘yan sandan Isokoko kan wannan lamari, inda suka kama Abdulrahman, sannan suka kai gawar Pelumi zuwa dakin ajiyar gawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce Abdulrahman yana hannun ‘yan sanda, inda kuma aka sake kama wasu mutane biyu duka akan wannan lamari.

Da yake mayar da martani akan cewa akwai yiwuwar za a saki Abdulrahman, Bala ya ce har yanzu suna cigaba da gabatar da bincike, idan aka kama Abdulrahman da hannu a kisan to tabbas za a gurfanar dashi a gaban kotu, idan kuma bashi da laifi za a sake shi. Ya ce ‘yan sanda suna gabatar da bincike akan gawar ta Pelumi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here