An kama daliban firamare maza da mata 35 tsirara suna shan kwayoyi da kwaroron roba masu yawa a tare da su

0
6705

‘Yan sandan kasar Kenya sun kama wasu daliban firamare dana sakandare guda 35 a wani samame da suka kai wani gidan haya a Sango Estate a cikin garin Homa Bay a ranar Juma’ar nan da ta gabata.

Yayin da 6 daga cikinsu suka gudu, an kama mata 20 da maza 15 da suke tsakanin shekaru 13 zuwa 17, inda aka same su a buge tsirara.

Haka kuma an samu kwaroron roba masu yawa da aka yi amfani da su a biyu daga cikin dakuna biyun dake gidan a wannan samame da suka kai.

Shugaban mutanen yankin Cif Robert Lango, ya ce iyayen wasu yara mata ne guda biyu suka kama gidan ga ‘ya’yansu, amma makwabtan gidan sun sanar da ‘yan sanda bayan kida ya dame su. Haka kuma an kama mai gidan da ya bayar da hayan shima.

Ya ce: “Mun samu kwaroron roba da muka tabbatar da cewa yaran ne suka yi amfani da shi wajen yin jima’i. Shida daga cikinsu sun tsere a lokacin da muka isa gidan.

“Wasu daga cikin yaran suna saka kayansu a lokacin da muka shiga gidan. Sun mayar da gidan mashaya.

“Na tattara mutane na muka je gidan. Mun rufe kofar gidan muka kira ‘yan sanda suka zo da mota kama su. Haka mai gidan shi ma an kama shi da ya kyale yara suka yi irin wannan abu a cikin gidanshi.”

Duka an dauke su zuwa ofishin ‘yan sanda na Homa Bay, amma daga baya an sake su saboda babu wajen da za a tsare su.

Kwamandan rundunar ‘yan sandan Sammy Koskey, ya ce tuni sun kira iyayen yaran akan su bayyana a ofishin ‘yan sandan a ranar Litinin 6 ga watan Yuli.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here