An hana masallata da suka je Masallaci babu takunkumi yin sallar Juma’a a Jos

0
335

Masallata da suka bijirewa dokar sanya takunkumi a garin Jos an hana su shiga Masallacin Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa mutanen da suka je Masallacin sanye da takunkumi a fuska an barsu sun shiga Masallacin, yayin da wadanda suka je babu takunkumi kuma aka dakatar da su a wajen Masallaci.

Wakilin Daily Trust din ya bayyana cewa tabbas ana bin dokar da gwamnatin ta sanya domin kuwa mutane na bin dokar tazara da aka bukaci su dinga yi.

A jiya Alhamis ne, gwamnatin tarayya ta fitar da ka’idoji na yadda za ayi sallar Juma’a, ciki kuwa hadda amfani da takunkumin fuska da kowanne Masallaci zai sanya idan har yana so yayi sallah a Masallaci.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan sallah ta Juma’a ita ce ta farko da aka gabatar tun a watan Afrilu da gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga ta kuma rufe wuraren ibada.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayyar ta kuma sanya dokar yin rijista ga dukkanin mutanen da za su ke zuwa wuraren bauta yin ibada don samun sauki wajen bin diddigi idan yiwuwar hakan ta taso.

Duka dai wannan wani yunkuri ne na gwamnatin tarayya wajen dakile yaduwar cutar coronavirus da har yanzu take addabar duniya ba tare da magani ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here