An gurfanar da kwamishinan jihar Kogi da ya yiwa budurwa fyade bayan bayyanar wani bidiyo

0
1048

Kwamishinan ruwa na jihar Kogi, Hon. Abdulmumuni Danga, wanda ake zargi da yiwa wata budurwa fyade, ya gurfana a gaban kuliya. Ko da yake, an samu matsin lamba daga gwamnatin jihar da kuma wasu ‘yan siyasa don karkatar da lamarin, in ji Segun Awosanya.

A farkon shekarar nan ne dai, wata budurwa mai suna Elizabeth, ta bukaci kwamishinan ya taimakawa ‘yar uwarsa da sauran danginsa da kudi.

Danga bai ji dadin wannan rubutu da budurwar tayi ba, sai ya dauko mata ‘yan daba suka sace ta da danta mai shekaru uku a duniya.

Bayan sun saki Elizabeth sai ta saki bidiyon yadda suka ji mata ciwo ta kuma zargi kwamishinan da yi mata fyade.

Elizabeth Photo Source: Linda Ikeji Blog

Elizabeth ta ce: “Bayan wallafa rubutun, sai suka fara zagina a shafukan sadarwa har ya turo ‘yan daba su kamani.

“Bayan sun kama ni sun yi mini duka, shi ma da kansa ya dake ni, ya cire mini kayana tsirara ya dauki bidiyona yayi mini barazanar zai wallafa shi idan na sake magana.

“Haka kuma sun tilasta ni na bayar da hakuri akan cewa abinda na fada ba gaskiya bane, tilas ta saka na rubuta na karyata kai na.

KU KARANTA: Shigar tsiraicin da kuke yi ne saka maza ke yi muku fyade – Likita ya dora laifin fyade akan mata

“Kwamishinan ya fasa mini wayata baki daya, inda yace akwai yiwuwar ina daukar bidiyon abinda suke yi.

‘Yan Najeriya dai sun nuna bacin ran su bayan Elizabeth ta wallafa wannan labari na ta, inda mutane suka dinga kira da a hukunta kwamishinan.

Fitaccen mai kare hakkin dan adam, Segun Awosanya, ya wallafa rubutu a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa an kama Danga a ranar Talata 2 ga watan Yuni, amma daga baya an sake shi bayan ya biya beli.

Segun ya ce an tattara bayanai masu yawa akan Danga wadanda suka sanya aka kama shi.

A wani bidiyo da yake yawo ya nuna lokacin da kwamishinan yaki yarda yayi bayani. Amma da ya gane cewa Segun yana wallafa bidiyon a shafukan sadarwa sai yayi.

“Yaki yarda yayi bayani inda yake nuna shi yafi karfin doka. Ni na kira kwamishinan ‘yan sandan jihar na gaya masa ya bayyana masa cewa duniya tana kallo,” cewar Segun, wanda yake bayani a shafinsa na Twitter.

Segun ya ce budurwar tana da shaida kwakkwara dake nuni da cewa kwamishinan ya ci zarafinta.

Haka kuma yayi zargin cewa akwai manyan mutane da suke so ayi watsi da shari’ar, wadanda suke goyawa Danga baya.

Ya ce: “Wannan lamari ne da yayi daban da sauran, amma lamari na fyade da ya kamata ya zama laifi a kowacce jiha. Abin takaici babban jami’in tsaro na jihar shi ne ke kokarin hana adalci. Magana ake ta shaida kuma mun da shaida mai yawa.

Daga baya yace an saki Hon. Danga akan cewa za a iya kiranshi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya ce: “Har yanzu bamu da masaniya akan belin shi da aka bayar, ba mu san wane dalili ne ya saka aka sake shi ba duk kuwa da wannan shaida da ake da su a kanshi. Haka kuma mun gano yadda gwamnan jihar da hukumar ‘yan sanda ta jihar ta shiga cikin lamarin saboda kawai rashin adalci. Muna kallo!”

Video Source: Linda Ikeji Instagram Page
Post Source: @segalink Twitter Page

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here