A wani bincike da aka gabatar na kayan tarihi da zamantakewa a kasar Madagaska an gano kasusuwan wata dabba wacce ta shekara miliyan 66 a duniya.
Binciken wanda aka wallafa a mujallar Nature ta masana kimiyya ya nuna cewa kasusuwan na wata dabba ce, wacce ta rayu lokaci daya da irin dabbobin Dinosors a yankin arewacin Madagaska.
Masu binciken sun sanyawa wannan kwarangwal suna ‘Adalatherium hui’, kuma sun bayyana cewa ba a taba samun dabba irinta ba.
A bayanan da binciken ya nuna, masanan sun gano cewa dabbar na da wasu irin hakora da ba a taba ganin wata halitta da take da irinsu ba, kuma dabbar ta rayu shekaru 66 a zamanin Kretase.