Sashe na goma na kwamitin gudanarwa ta harkokin shari’ah a kasar Turkiyya ta soke hukuncin da kotu ta yanke a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 1934, wanda ya bada damar mayar da babban Masallacin Juma’a na Hagia Sophia zuwa gidan ajiye kayan tarihi.

Wata kungiya ta adana kayan tarihi da yiwa muhalli hidima ce ta shigar da wannan kara, inda ta nemi kotun da ta soke matakin da majalisar ministocin kasar ta saka na mayar da Masallacin gidan tarihi.

Bayan gabatar da nazari mai zurfi, kwamitin gudanarwar ta harkokin shari’a a kasar ta Turkiyya ta soke wannan hukunci da aka yanke a baya.

Kwamitin shari’ar ta ce Masallacin Hagia Sophia, mallakar asusun Sarki Sultan Mehmet Hanne ne, dan haka wurine da yake taimakawa jama’a matuka.

Hagia Sophia | Photo Source: TRT Hausa

Bayan haka kuma takardun wannan wuri na mallaka sun nuna cewa Masallaci ne na Juma’a da ake gabatar da ibada a ciki.

Babban mai taimakawa shugaban kasar Turkiyya a fannin sadarwa, Fahrettin Altun ya sanar da cewa shugaban kasar Erdogan zai yiwa ‘yan kasar jawabi da karfe 8:55 na daren jiya Juma’a.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here