An ceto ‘yammata 69 ‘yan Najeriya da aka yi safarar su zuwa kasar Lebanon aka mayar da su bayi

1
597

An samu nasarar ceto rayukan wasu ‘yammata guda hamsin da aka yi safarar su zuwa kasar Lebanon, da kuma wasu mutane 19 suma ‘yan Najeriya da rayuwa tayi musu wahala a kasar.

Ministan kasashen waje, Geoffrey Onyeama, shine ya bayyana haka inda ya ce an dawo dasu duka Najeriya a jiya Lahadi.

Ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon da kuma ‘yan Najeriya dake kasar wajen kokarin da suka yi aka dawo da mutanen gida Najeriya.

“Tare da taimakon kudi da kayayyaki da gwamnatin kasar Lebanon ta bayar, mun samu damar dawo da ‘yan Najeriya guda 50 da aka yi safarar su zuwa kasar da kuma mutane 19 ‘yan Najeriya da suka shiga wani hali a kasar.” Cewar shi.

“Muna mika godiyar mu ga jakadan kasar Lebanon na Najeriya Houssam Diad, da kuma jakadan Najeriya dake kasar Lebanon Goni Zannabura, dama sauran ‘yan Najeriya dake kasar Lebanon.”

Wannan rahoto ya zo ne dai makonni kadan bayan an ceto wata budurwa ‘yar Najeriya dake kasar Lebanon din da aka sanyata a kasuwa za a sayar a shafin sada zumunta na Facebook.

A ranar 28 ga watan Afrilu, 2020, budurwar mai suna Peace Ufuoma, wacce aka yi safarar ta zuwa kasar an gano ta a shafin Facebook bayan wani dan kasar Lebanon mai suna Wael Jerro ya sanyata a kasuwa, inda cikin gaggawa gwamnatin Najeriya ta sanya baki aka ceto ta.

Haka kuma gwamnatin kasar Lebanon ta cafke Jerro.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here