An ceto rayuwar budurwa ‘yar Najeriya da aka sayar da ita $1,000 a kasar Lebanon

0
373

An ceto rayuwar budurwa wata budurwa mai suna Busari Peace, wacce a makon da ya gabata wani dan kasar Lebanon mai suna Wael Jerro, ya sanya tallarta a shafin Facebook akan kudi $1,000, kimanin naira dubu dari uku da sittin kenan.

Sanarwar ta fito daga bakin shugabar ‘yan Najeriya dake kasashen waje, Abike Dabiri Erewa.

Jerro wacce aka sanya hotonta a shafin Facebook domin sayar da ita, inda mutumin ya bayyana cewa ‘yar aiki ce, ya kuma bayyana cewa zai sayar da ita akan kudi $1,000, tuni dai yanzu an cafke shi.

Dabiri, Erewa, wacce ta wallafa haka a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa yanzu haka Peace tana ofishin jakadancin jakadancin kasar dake Beirut.

“Sanarwa dangane da budurwa ‘yar Najeriya da aka sanya ta a kasuwa a kasar Lebanon a shafin Facebook, yanzu haka an ceto ta tana ofishin jakadancin Najeriya dake Beirut.” Cewarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here