An cafke matashi da yake kokarin sace yaro dan shekara 2 a Kano

0
389

A jiya Asabar ne aka kama wani matashi mai shekaru 20 a duniya, a lokacin da yake kokarin yin garkuwa da wani yaro mai shekara biyu a duniya akan titin Aba, dake Sabon Gari cikin birnin Kano.

An ruwaito cewa ‘yan sanda ne suka ceto rayuwar saurayin daga hannun matasa wadanda suka kama shi a lokacin da yake shirin sace yaron.

Saurayin wanda aka boye sunanshi, ya shiga wani gida mai bene hawa daya, inda ya dauko yaron, amma asirin shi ya tono a lokacin da yake hanyar fitowa daga gidan, inda wani makwabcin gidan ya ganshi da yaron.

Cikin gaggawa ya sanar da jama’a, inda aka kama matashin ake shirin sanya masa wuta. An samu jikin shi cike da guraye da layu, wadanda yake tunanin zasu taimaka masa a hali irin wannan, sai dai a wannan karon sun bashi kunya.

Daga baya jami’an tsaro sun isa wajen suka karbe matashin suka tafi dashi ofishinsu dake Nomandland domin cigaba da bincike a kanshi.

Sai dai har ya zuwa yanzu dai ba aji ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, game da lamarin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here