An bukaci a kori Isa Ali Pantami daga mukamin shi kan zargin cin zarafin mata da yayi

8
5438

Kungiyar marubuta ta kare hakkin dan adam ta Najeriya (HURIWA) ta zargi kungiyar kare hakkin mata ta Najeriya da nuna halin ko in kula akan abinda ministan sadarwa, Isa Ali Pantami ya yiwa mata akan rikicin ofis.

Kungiyar ta ce abin takaici ne ace irin wannan mummunan zargi na nuna wariya ga mata da mai bawa shugaban kasa shawara akan ‘yan Najeriya dake kasashen ketare, Mrs Abike Dabiri-Erewa tayi akan ministan sadarwar, tsawon kwanaki uku babu wata kungiya da ta fito ta nuna rashin jin dadinta.

A wata sanarwa dauke da sa hannun babban jami’in hulda da jama’a na kasa Emmanuel Onwubiko da kuma daraktar harkokin watsa labarai ta kasa, Zainab Yusuf, HURIWA ta ce taga irin rikicin dake faruwa tsakanin ministan sadarwa na Najeriya da shugabar kungiyar ‘yan Najeriya dake kasashen ketare, wanda ya samo asali akan ofis, amma duk da haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ko wata kungiya ba ta fito tayi magana akan wannan batu na wariyar jinsi ba.

Kungiyar ta ce sashe na 42 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta nuna wariyar launin fata ko kuma wariyar jinsi, saboda rashin tunani ne a bar wanda yake nuna kiyayya ga mata ya rike mukami a gwamnati.

“Maganar gaskiya barin mutum wanda bashi ganin darajar jinsin mutane ya cigaba da rike mukamin gwamnati alamu ne na nuna rashin bin doka,” cewar kungiyar.

HURIWA ta bayyana cewa rikicin dake tsakanin jami’an gwamnatin ya bayyana ne bayan NIDCOM ta wallafa bidiyon da aka dauka a watan Fabrairu a shafinta na Twitter inda ta zargi Pantami da hannu wajen korar mutane daga ofishin nata dake Abuja.

HURIWA tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi bincike akan wannan zargi na wariyar jinsi da Abike Dabiri tayi akan ministan sadarwar, inda ta bayyana cewa idan har an same shi da hannu a ciki a cire shi daga mukamin.

HURIWA ta kara da cewa idan ma’aikatar raya mata ta Najeriya ba ta nuna hali na dattaku ba wajen fitowa tayi Allah wadai da wannan abu da hankalinsu ba zai kawo kan lamarin ba, amma yanzu ta gane cewa ma’aikatar wurine da kawai ake bawa mutanen da suke nuna goyon bayansu ga shugaban kasa ayyukan yi ba wani abu ba.

8 COMMENTS

 1. A gaskia idan aka zargi ministan sadarwa da rashin sanin mutun jansi anyi jahilcin gaske dan a zahirin gaskia tsare mutuncin kasa yake da kuma na matan

 2. Nifa haryanxun ban fahinci zahirin laifinda akecewa yayiba dan haka Allah ya karya duk mai adawa da pantami a duniyarnan na bayyane da na boyema daga karshe mutafatan Allah yakara karemanakai malam masu adawa dakai Allah yashiryesu inba masu shiryuwabane Allah kafimu Sanin yadda zakayidasu

 3. Kude inba fasiki aka kawoba bazaku ji dadiba.
  Duk murumin daya suffantu da addini sai kun muzantashi gabadaya a maganganun babu ingredients sai kamekame kawai to kusani zakumutu shima zaimutu duk sai Allah yataraku agabansa sannan yemuku hukunci

 4. Idan kuna maganar kundi n tsarin kasa
  Shifa na musulunci kuma wlh dukkan musulmi insha allahu muna tare da pantami suna fadane kawai da suma fadane kawai mudulunci

 5. Wannan fakewa da guzuma ne aharbi karsana.
  Tunda shi Mallam pantami malamin addinine kuma na musulunci, sai sufake dawannan cewa ai musulunci baya girmama jinsin Mata, daman akan haka suke. Azahirin gaskiya in dai yadda na karanta labarin haka take, ton banga abinda yahadashi da cin zarafin mataba, toh idan ace namiji ne shugabantar mukaminta, sai shikuma ace anci zarafin maza? Wannan dai ta canza wani zargin dumin wannan bai karbuba

 6. Amma dai mutane suncika jahilci da yawa ko dai son rai ne ko ince nuna rashin so musulunci a fili,me yahada rikicin office da cinzarafin Mata.
  Kawai dai angayana wakilta musulmai da musulunci shiyasa ake alkanta rikicin da cinzarafin Mata saboda abata ma musulunci da malan suna tunda ya tsare gaskiya.

 7. Allah yana bayan mai gaskiya,, babu abinda zai faru da pantami sai alkhairi inshallah,, banda kame kame babu abinda sukeyi . Ai duk wanda ya zargi mal. Akan nuna banbancin jinsi baiyi masa adalci ba. Fatarmu shine ace gwamnati ta kawo mana ire irensu pantami

  • No Ina ganin wannan zancen banzane domin bansan abinda yahada rikicin office ba da cin zarafi kokuma sun jahilci kalmar cin zarafinne Allah ya kyauta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here