An bude Masallatai a kasar Iran don cigaba da bautar Allah duk da fama da Coronavirus da suke yi

0
541

A ranar Litinin dinnan ne aka bude Masallatai a wasu bangarori na kasar Iran inda aka samu saukin annobar Coronavirus, yayin da ta bayyana mutuwar mutane 74 a kasar sanadiyyar cutar.

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya na kasar Kianoush Jahanpour, shine ya bayyana haka, inda yace sababbin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar ya saka yawan wadanda cutar ta kashe ya kai mutane 6,277 a kasar tun lokacin da cutar ta bulla kasar.

Haka kuma an kara samun mutane 1,223 da suka kamu da cutar ta Coronavirus a kasar a cikin kwanaki 24, cewar jahanpour, inda yawan masu cutar ya kai 98,647.

A yanzu haka an bude Masallatai domin a cigaba da ibada a wasu bangarori na kasar da aka samu raguwar yaduwar cutar.

An fara amfani da kala a kasar irinsu fari, ruwan dorawa da ja, domin banbance wuraren da suke da hadari da kuma inda babu.

Mutane zasu shiga Masallaci da takunkumin hanci da kuma safar hannu, kuma zasu yi sallah tsawon mintuna 30 ne kawai.

A cewar Jahanpour, mutane 79,387 da aka kwantar a asibiti sanadiyyar cutar tun bayan bullarta a kasar a tsakiyar watan Fabrairu an sallamesu, inda mutane 2,676 suke cikin mawuyacin hali.

Ya bayyana cewa kasar Iran tana daya daga cikin kasashe guda biyar na duniya da suka fi yawan wadanda suka warke daga cutar.

Sai dai kuma masana da wasu manyan mutane na duniya suna ganin mutanen da suke da cutar a kasar yafi wanda gwamnati take fada.

AFP

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here