An bayyana dalilin da ya saka shugaba Buhari baya saka takunkumin fuska (Face Mask)

0
165
  • Manyan hukumomin lafiya da masana a fannin kimiyya sun bukaci kowanne mutum ya dinga sanya takunkumin fuska don kare kanshi da wasu daga kamuwa da cutar Coronavirus
  • To sai dai tun bayan bullar cutar ta coronavirus a Najeriya, an sha ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da takunkumi ba, hakan ya sanya wasu ke magana
  • Babbar mai taimakawa shugaban kasa a fannin sada zumunta ta musamman, Lauretta Onochie tayi bayanin dalilin da ya sanya shugaban kasar baya amfani da takunkumin

Mai taimakawa shugaba Buhari ta musamman a fannin sada zumunta, Lauretta Onochie, ta bayyana dalilin da ya sanya shugaban kasar baya sanya takunkunmin fuska, wato ‘Face Mask’ a turance.

Hukumar NCDC, ma’aikatar lafiya, da kuma kwamitin lura da cutar Coronavirus, sun shawarci ‘yan Najeriya da su dinga sanya takunkumin fuska domin gujewa kamuwa da cutar Coronavirus.

A lokuta da dama an gano shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da takunkumin fuska ba tun bayan lokacin da annobar ta kunno kai, kuma hotuna da dama da ake dauka sun nuna shugaban kasar ne kadai yake zaune ba tare da takunkumi ba.

Da take kare shugaban kasar, Onochie ta bayyana cewa masana a fannin lafiya sun bayyana cewa ba dole sai anyi amfani da takunkumin fuska ba indai har ana da tabbacin wurin da ake babu matsala, kuma wannan dalilin ne ya sanya shugaba Buhari ya daina sanya takunkumin.

A rubutun da ta wallafa a shafinta na Twittr, Onochie ta bayyana cewa shugaban kasar bai karya doka ba kan kin sanya takunkumin. Ta ce dokar ta nemi wadanda zasu kawo ziyara ne su sanya takunkumin domin tabbatar da basu kai cutar wajen da suka je ba.

“Shugaba Buhari bai karya kowacce doka ba, masana a fannin lafiya, sun ce idan mutum na zaune a wajen da babu matsala ba dolene sai ya saka takunkumi ba.

“Amma wadanda za su kai masa ziyara dole sai sun saka takunkumi, don tabbatar da cewa basu yada cutar ba.

“Saka takunkumi muna yi saboda mu kare mutanen da suke kusa damu ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here