Amaechi ya bayyana wani abu guda daya da ya kasa ganewa dan gane da shugaba Buhari

1
542

Da yake magana akan yanayin aikin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawon shekara biyar, ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yayi magana akan tsarin mulkin shugaban kasar a wannan lokaci.

Da yake hira da gidan talabijin na NTA a safiyar yau Juma’a, 29 ga watan Mayu, Amaechi ya ce abinda yake daure masa kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari shine shirun da yake yi dangane da nasarar da gwamnatinsa take samu akan sabon tsarin mulkin da yake tafiyarwa a Najeriya.

Ministan ya ce zancen gaskiya shugaba Buhari bai damu da yin surutu ba akan ayyukan da yake yi ko ya saka a gaba, saboda haka yasa baya magana kawai ya mayar da hankalinshi wajen yin aiki, ya kara da cewa wanna hali da shugaban kasar yake dashi yana ba shi mamaki, inda ya ce hatta sauran ministoci suna mamaki sosai.

A zahiri, tsohon gwamnan jihar Ribas din ya bayyana cewa, idan har shugaban kasar yana son ganawa da wani babban mutum a Najeriya, baya wuce minti uku kacal ake shawo kanshi game da aiki da zai amfani Najeriya.

A daya bangaren kuma Press Lives ta kawo muku rahoton hirar da aka yi da babban mai bawa shugaban kasa shawara a fannin sadarwa, Malam Garba Shehu, akan cigaban da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo wa Najeriya a shekaru biyar da yayi akan mulki.

Malam Garba Shehu ya ce tabbas ya san cewa ba wai sun cimma gaci bane a cikin abubuwan da suka lissafa za su yiwa ‘yan Najeriya, amma yana da tabbacin cewa sun ciyar da kasar gaba fiye da yadda suka iske ta.

Ya kum kara da cewa dama canji mai dorewa ba wai yana samuwa a lokaci daya bane, dole sai a hankali, kuma ba wai sunce za su cikawa talakawan Najeriya alkawuran zabe a cikin shekara biyar dari bisa dari bane.

1 COMMENT

  1. Gaskiya ne, babu musu. Duk mai hankali yasan sun ciyar da kasar nan gaba waje lalacewa, wajen tilasta sakin aure, wajen tilasta shaye shaye, sace, sace, zinace, zinace. Duk wani abu da ka sani yake da wahalar yiwuwa na lalacewa a kasar nan, a lokacin su ya zama sassauka wajen aiwatar da shi. To muna rokon Allah da ya azurta ku da irin wannan cigaban a makwancin ku, wato kabari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here