Almajirai 16 da aka debo su daga jihar Kano aka kawo su jihar Kaduna an same su da cutar Coronavirus

0
135

Almajirai 16 da aka debo su daga jihar Kano aka kawo su jihar Kaduna an same su da cutar Coronavirus.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, ya ce wannan ya nuna matsalar dake tattare da jihohin dake makwabta da jihar, da kuma zirga-zirga tsakanin wata jihar zuwa wata jihar.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta kara samun wasu mutane 16 da suke dauke da cutar a jihar. Wadanda cutar ta harba duka almajirai ne da suka dawo daga jihar Kano, hakan ya saka yawan mutanen dake dauke da cutar ya karu zuwa 25 a jihar.”

“Yawancin mutanen da suke dauke da cutar suna da alaka da dawowa daga wata jihar, ma’ana ba jihar Kaduna suka dauki cutar ba, hakan ya sanya gwamnatin jihar Kaduna take tsoron matsalar da jihohin dake makwabtaka da ita za su jawo, da kuma tafiye-tafiye zuwa wasu jihohi, za su taimaka wajen yaduwar cutar,” ya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here