Allahu Akbar: ‘Yar gidan babban dan siyasa a kasar Italy ta Musulunta ta canja sunanta zuwa Aisha

0
533

‘Yan kasar Italiya sun cika da mamaki bayan ‘yar gidan dan majalisa a kasar ta bayyana fitar ta daga addinin Kiristanci zuwa addinin zuwa addinin Musulunci, inda kuma ta canja sunanta zuwa Aysha.

Kyakkyawar budurwar mai suna Manuela Franco Barbato budurwa ce mai shekaru 22 a duniya da take karatu a jami’ar L’orientale de Napoli. Diya ce ga Franco Barbato, tsohon dan majalisar kasar.

Mahaifinta ya bayyanawa manema labarai cewa: “Komawarta addinin Musulunci ba karamin kadasu yayi ba, basu ji dadi ba ko kadan. Ina matukar bakin ciki da wannan rayuwar da ta zabawa kanta.”

Bayan komawarta addinin Musulunci tayi rubutu kamar haka a shafinta na Facebook: “Hijabi shine Allah ya zaba mini, ina matukar tinkaho da tsarkake zuciyata da Allah yayi. Wannan ita ce shari’ar Allah, wacece ni da zance ba haka ba?” Wannan rubutu da tayi ya jawo kace-nace matuka a shafukan sadarwa, inda ‘yan kasar ta Italiya da suke yiwa addinin Musulunci fahimta ta daban suka dinga fadar albarkacin bakinsu.

Allah yayi mata albarka ya kuma cigaba da yi mana jagora.

1 COMMENT

  1. Hakafa rayuwar take..Man Amila Salihan Fali Nafsih’ Waman Asa’a Fa Alaiha Summa Ila Rabbikum Turja’uuun..

  2. Masha Allah,welcome to new life sister ,may Allah blessing you and protect you more against enemies in the world, masha Allah sister to new life in inslam way

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here