Allahu Akbar: Shigowar Sarauniyar kyau ta duniya addinin Musulunci ya jijjiga duniya

0
588

Kwarai kuwa addinin Musulunci shine addini mafi girma da ni’ima. Shine addini mafi sauki, hakan ya sanya miliyoyin mutane ke komawa addinin Musulunci. Bayan haka babu wani addini da Allah zai yi amfani da shi a ranar lahira idan ba addinin Musulunci ba.

“Kuma duk wanda yayi wani addini wanda ba addinin Musulunci ba, baza mu saurare shi ba, haka kuma a lahira yana daga cikin masu asara.” (Qur’an 3:85).

A kowacce rana muna ganin daruruwan mutane suna karbar addinin Musulunci kuma suna zaune cikin jin dadin rayuwa.

A wannan karon zamu kawo muku labarin sarauniyar kyau da ta karbi addinin Musulunci. Ta karbi addinin Musulunci cikin farin ciki, kuma ta karbe shi da gaske domin kuwa har hijabi take sakawa.

Ba kowa bace wannan face tsohuwar sarauniyar kyau ta kasar Czech Republic, Marketa Korinkova.

Marketa Korinkova ta karbi addinin Musulunci bayan ta tuba ta fita daga addinin Kiristanci. Ta ce ta yanke shawarar karbar addinin Musulunci ta koma kasar Dubai da zama ta bar kasarta ta haihuwa.

Bayan haka Marketa ta canja sunanta zuwa Maryam. Ta ce karrama mata da addinin Musulunci yayi ya sanya ta karbi addinin Musulunci. Ta ce ta shafe shekara uku tana tunanin karbar addinin Musulunci. Ta bayyanawa duniya kowa ya sani cewar ta Musulunta a kasar Dubai.

A rahoton da Arab Journal ta ruwaito a birnin Landan, fitacciyar budurwar wacce tayi suna a duniya, Marketa Korinkova ta baiwa masoyanta mamaki matuka bayan ta bayyana cewa ta Musulunta. Marketa ta lashe gasar sarauniyar kyau ta duniya da aka gabatar a kasar Italy, inda tun daga wannan lokacin tayi suna sosai a duniya.

Manyan kamfanoni na duniya sun bukaci amfani da hotonta wajen tallata kasuwarsu. Haka kuma masana’antar fim ta kasar Amurka, Hollywood ta bukaci ta fara sanya ta a cikin fim. Banda manyan kamfanoni na duniya da suka dauketa suke yin talla da ita a kasashen Dubai, Amurka, Prague da sauransu.

Tayi karatunta na Digiri a fannin Turanci a jami’ar Charles dake kasar Prague. Daga baya tayi Digiri na biyu a birnin Landan.

Bayan ta samu nasarar lashe sarauniyar kyau, Allah ya daukaka ta a duniya, amma ta ce duk da wannan daukaka da ta samu bata jin farin ciki a ranta. Tayi duk abinda ta ga ya kamata tayi domin ta kawar da damuwar amma damuwar taki tafiya.

Bayan shawarar daya daga cikin abokanta, sai ta fara koyar addinai kala-kala shekaru uku da suka wuce. Duk da cewa Kiristanci shine addininta, amma ta kasa samun kwanciyar hankali da shi. Sai ta fara bincike akan addinin Musulunci. Allah ya bude mata idonta sai ta yanke shawarar karbar addinin Musulunci.

Bayan kwashe shekaru a kasar Dubai sai ta yanke shawarar zama a kasar baki daya.

Ta ce a lokacin da take yarinya an bayyana mata addinin Musulunci bai bawa mata ‘yanci ba ko kadan. Amma bayan tayi bincike kan addinin Musulunci sai ta gano gaskiyar cewa addinin Musulunci shine addinin da yafi kowanne addini bawa mata ‘yanci.

A lokacin da ta wallafa hotonta sanye da hijabi, miliyoyin mutane sunyi ta mamaki. Sun dauka cewa ta samu talla ne da ya sanya dole sai ta sanya hijabi. Bayan ta bayyana musu cewa ta Musulunta sai suka cigaba da mamaki.

Yanzu haka tana zaune a kasar Dubai tana cigaba da nuni ga addinin Musulunci akan shine addinin gaskiya.

Allah ya kara mana imani, nauyi ne akan kowa ya yada kalmar Allah ga sauran mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here