Allahu Akbar: Mahaifiyar shugaban sojojin Najeriya Tukur Buratai ta rasu bayan fama da rashin lafiya

0
110

A jiya Talata ne Hajja Kakah, mahaifiyar shugaban sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai, ta koma ga Allah a jihar Borno.

Wani dan gidan ne ya bayyanawa Sahara Reporters labarin rasuwar ta, bayan ta sha fama da rashin lafiya a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

“Kwarai kuwa ina tabbatar muku da cewa ta rasu.

“Ta rasu yau Talata da daddare kuma za ayi jana’izarta ranar Laraba da misalin karfe 8 na safe. Allah ya jikanta yayi mata rahama.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here