Allahu Akbar: Kyakkyawar budurwa ‘yar gidan wani mai fada aji a kasar Australia ta Musulunta

0
1621

Tabbas Musulunci yana jawo mutane cikin shi a kowacce rana. Ko shakka babu Musulunci shine addinin da yafi kowanne yaduwa a duniya a wannan lokacin.

Musulunci ya bawa mabiyansa wasu abubuwa da wasu addinai basu bayar ba, saboda Musulunci shine addinin da Allah ya aiko daga sama.

‘Yar gidan wani dan majalisa a kasar Australia ta Musulunta a lokacin da take da shekaru 19 a duniya. A baya tayi abubuwa marasa dadin ji, amma yanzu ta sha alwashin zama Musulma ta gari.

Kyakkyawar budurwar mai suna Brianna Costigan, diya ce a wajen dan majalisar birnin Queensland, Jason Costigan. Brianna tayi tu’ammali da miyagun kwayoyi a baya da wani Musulmi wanda a yanzu shine mijinta da suke zama a birnin Sydney.

Kafin Brianna ta karbi addinin Musulunci tayi rayuwa marar dadin ji, tayi harkar safarar kwayoyi. Mutane sunyi matukar mamaki a lokacin da ta wallafa hotonta sanye da hijabi tana yabon Allah.

Ta kuma goge duka abubuwan da ta wallafa a shafukanta na sadarwa, inda tayi wani rubutu da ya jawo hankalin mutane ta ce: “kada ka tambayi abinda Allah ya tsara. #alhamdulillahforeverything.”

Brianna ta auri Ahmed Taha sannan ta Musulunta. daliba ce a fannin shari’a a jami’ar New South Wales dake kasar Australia.

Ta bayyana a gaban kotu shekarar da ta gabata a lokacin da ake zarginta da safarar hodar ibilis. Ita da mijin nata na yanzu duka an yanke musu hukuncin safarar miyagun kwayoyi.

An kama ta a shekarar da ta gabata, bayan ta sayar da kwayar ga wasu jami’an tsaro da suka yi badda kama.

Sai dai lauyan ta ya bayyana cewa duk da dai an kamata tana yin wannan harkalla amma ba ita ba ce ta hada wannan harka.

Sai dai a yanzu ta manta da komai ta rungumi addinin Musulunci. Duk da dai Allah ya fi mu sanin abinda ke boye, amma zamu iya yi mata fatan alkhairi ita da mijinta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here