Allahu Akbar: Kauye guda na Kiristoci sun karbi Musulunci a kasar Philippines

0
1631

Mutane na Musulunta a lokuta da dama. A wasu lokutan mutum na samun koyarwar Musulunci a saukake sai ya karbi addinin ba tare da wani ja in ja ba.

Amma idan ana maganar mutane masu tarin yawa, da wahala a kira su duka zuwa hanya guda daya. Wata kungiya ta Musulmai masu Da’awah sun sami nasarar Musuluntar da wani kauye na Kiristoci zuwa addinin Musulunci a kasar Philippines.

Duka al’ummar tsibirin Banyatan dake Cebu-Philippines sun karbi addinin Musulunci bayan kungiyar masu Da’awar ta kai ziyara kauyen ta kuma kira su zuwa Musulunci.

Kungiyar mai suna ‘British Islamic Organization’, ma’ana ‘Kungiyar Addinin Islama ta Birtaniya’, ta yi wannan aiki ne bayan sun nunawa mutanen kauyen matsayin Annabi Isa a cikin Qur’ani.

Lamarin ya samo asali ne a lokacin da Abu Bakr, wani matashin Kirista da ya Musulunta da ya gina Masallaci a garin ya kira kungiyar Da’awar zuwa kauyen domin yin wa’azi ga al’ummar kauyen.

Kafin ‘yan kungiyar su fita wannan aiki, sun sayi kayan abinci masu tarin yawa ga talakawa mazauna kauyen da taimakon Abu Bakr. Bayan wannan sun fara tattaunawa da su dangane da Annabi Isa.

Sun kuma yi musu bayani yadda Annabi Muhammad (SAW), ya nuna cewa al’ummar Musulmai suyi imani da Annabi Isa da mahaifiyarsa Maryam, amma kuma Musulunci ya hana bautar gumaka, giciye, duwatsu, itatuwa, mutane, aljanu, mala’iku da annabawa.

Wannan tattaunawa da muhawara da aka yi yayi tasiri a zuciyar mutanen kauyen, inda suka yanke shawarar bin gaskiya kuma suka Musulunta baki daya.

“Wannan abu ne na farin ciki, yayin da duka kauyen suka Musulunta a matsayin al’umma daya,” inji daya daga cikin masu da’awar.

Duka mutanen kauyen wadanda yawansu ya kai mutum 215 sun karbi kalmar Shahadar cikin yanayi na ban sha’awa.

Kasar Philippines wacce yawancin mutanen cikinta Kiristoci ne, inda kashi 8 cikin dari ne kawai Musulmai a kasar. Yawancin Musulman kasar suna zaune a Mindano da wasu yankuna na kusa da su.

A zamanin da yawancin mutanen kasar Musulmai ne, amma a lokacin da kasar Spain ta kai hari ta kafa daularta a can, sai suka mayar da mutanen kasar zuwa addinin Katolika. Yana da muhimmanci kowa ya sani cewa wadannan mutanen da suke zaune a Philippines suna da tarihin addinin Musulunci.

Hakan ya sanya a lokacin da Musulunci ya kara zuwa wajensu, suka karbe shi hannu biyu-biyu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here