Allahu Akbar: Idan har Musulunci zai sanyaki farin ciki kije ki Musulunta – Cewar Kirista da ya goyi bayan Musuluntar ‘yarshi

0
1318

Canja addini zuwa wani addini ya zama abu da aka jima ana yi shekara da shekaru. Duk da dai mun san cewa addinin Musulunci shine addini na gaskiya.

Amma a lokuta da dayawa mutanen da suke shigowa Musulunci suna shiga wani hali da yake sanyawa wani lokacin dole sai sun abr iyayensu, kadan ne iyayensu suke basu goyon baya wajen Musulunta.

Wannan labarin wata kyakkyawar budurwa ne ‘yar kasar Singapore, wacce ta Musulunta kuma iyayenta suka goyi bayanta.

Budurwar mai suna Li Jinghan wacce ta Musulunta ta bayyana labarinta a shafin Facebook, inda ta bayyana yadda mahaifinta ya nuna goyon bayanshi akan Musuluntar ta.

A rubutun da ta wallafa wanda ta sanyawa suna ‘hira tsakanin mahaifinta da dan kasar Malaysia’ inda mahaifinta ya bayyanawa mutumin dalilin da ya sanya ya amince ‘yarshi ta Musulunta.

Ta ce:

“Makon da ya wuce mahaifina ya tambayeni ko zan iya siya mishi abu a yanar gizo, na saya mishi. Ai kuwa sai na tura masa da adireshin shagon domin yaje ya karbo.

“A lokacin da ya isa shagon, mai shagon wanda yake dan kasar Malaysia ne, mai shagon yayi mamaki da yaga mahaifina, domin yayi tsammanin zai ga dan kasar Malaysia ne.

Mai shagon ya ce masa ya aka yi na ganka, ya ce masa nice na siya abin shi yazo dauka ne, sai ya ce masa to ai ni ina sanya Hijabi. Sai ya tambayi mahaifina shin shima Musulmi ne?

“Ya ta Musulma ce, ta Musulunta. Ya aka yi ka bari ta Musulunta? Baka yi kokarin hana ta ba? Cewar mai shagon.

“Ina goyon bayanta, mahaifina ya ce.

‘Gaskiya babu ruwana, ya aka yi ka goyi bayanta?”

“Mahaifina yayi dariya a lokacin da yake sanar dani labarin, ya ce ya kasa gane mai yasa mutane suke mamaki idan suka ji labarin Musulunta ta.

“Sai na ce masa, saboda irinku baku da yawa. Shin mai yasa ka bari na Musulunta?

“Saboda na riga na san yadda rayuwa take, cewar mahaifina.

“Saboda na san yadda neman farin cikin rayuwa yake, menene amfanin rayuwa? Shi ne mutum ya samu abinda ke sanya shi farin ciki.

“Mutane da yawa suna samun farin ciki a abubuwa daban-daban. Wasu a dukiya, wasu a dangi, wasu kuma a addini.

“A matsayinmu na iyaye za mu so muga ‘ya’yanmu cikin farin ciki. Kowanne addini yana koyar da abu mai kyau.

“Idan har wannan addinin zai sanya ki farin ciki, wane dalili ne zai saka na hanaki?

“A lokuta da dama ina ganin mahaifina yana da saukin kai. Duka abubuwan da ya fada haka suke; Zai yi wuya ka samu wani wanda zai iya yin irin wannan bayani nashi, maganar gaskiya da yawa ma baza su bari ma haka ta faru ba.

“Babu ruwanshi da abinda mutane za su ce, ko kuma abinda ‘yan uwanmu za su ce, abinda yafi damuwa da shi shine farin cikina.

“Ina jin hakane ya sanya nake daukar maganarshi da muhimmanci, saboda in dai ya fadi abu to haka yake nufi har cikin zuciyar shi.

Yanzu dai budurwar mai shekaru 29 ta canjawa kanta suna zuwa Nur Jihan Li, kuma tana zaune cikin jin dadi da iyayenta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here