Allahu Akbar: Fitaccen Jarumin Hollywood Vin Diesel ya yabi watan Ramadana mai albarka a cikin wani bidiyo

1
212

A wannan lokaci na yanar gizo da fasahar shafukan sada zumunta, abubuwa da yawa ka iya yaduwa su jawo hankalin miliyoyin jama’a.

A wani bidiyo da ya gama yaduwa a kafafen sadarwa, fitaccen jarumin masana’antar fina-finan kasar Amurka ta Hollywood, Vin Diesel an nuno shi yana yabon watan Ramadana mai alfarma, inda har yake bayyana cewa shima zai yi azumin.

A bidiyon wanda ya nuna fitaccen jarumin da kuma wani fitaccen mawaki dan kasar ta Amurka, mai suna French Montana, wanda yake shi dama Musulmi ne, ya dauki hankalin al’umma sosai.

Bidiyon wanda French Montana ya wallafa a shafinsa na Instagram, an jiyo Vin Diesel yana cewa, “tsarin watan Ramadana abu ne mai girma” inda ya kara da cewa “yana iya yiwuwa tsarin yana da kyau ga rayuwar kowanne mutum.” Ya bayyana irin jajircewar da watan yake sanya Musulmai suyi a matsayin hanyar karfafa imani.

Bidiyon ba wai sabon bidiyo bane, inda a yanzu haka yayi wajen shekara uku da aka dauke shi, kamar yadda shafin French Montana na Instagram ya nuna.

Ranar da aka dauki bidiyon ba wai shine abin duba ba, sai irin kallon da wannan fitaccen jarumi yake yiwa addinin Musulunci shine abu mafi ban sha’awa.

A daya bangaren za’a ga French Montana yana gayyato jarumin domin ya taya al’ummar Musulmai murnar watan Ramadana.

Muna rokon Allah ya ganar da jarumin ya kuma yi mishi jagora zuwa addinin Musulunci.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here