Allahu Akbar: Faston kasar Amurka ya Musulunta bayan ya samu tarba ta musamman a kasar Saudiyya

0
2106

Wani babban fasto na kasar Amurka ya Musulunta bayan ya samu tarba ta musamman a kasar Saudiyya a lokacin da ya kai ziyara kasar.

Samuel Earle Shropshire ya fara zuwa birnin Jeddah a shekarar 2012, inda yaje yayi aiki a matsayin edita na Al-Qur’ani mai girma da za a fassara.

Da farko yana ta faman wasu-wasi akan aikin saboda irin kallon da yake yiwa addinin Musulunci dama Larabawa baki daya. Sai dai daga baya ya gano cewa kafafen sadarwa basa nuna ainahin abinda ake nufi da Musulunci.

Samuel Earle Shropshire ya bayyana hakane a wata hira da yayi da wasu jami’an kasar ta Saudiyya a shafin labarai na yanar gizo na Sabq.

Faston mai shekaru 70 ya bayyana cewa a lokacin da ya fara zuwa birnin Jeddah a shekarar 2012 lokacin da zai yi aiki a matsayin edita, ya damu sosai saboda kallon da yake yiwa Musulmai a wancan lokacin.

“Daga baya na gano cewa abinda nake gani a kafafen sadarwa da kuma ji ba gaskiya bane,” ya ce.

“Na ga mutanen kirki, wadanda basu damu ba ko kadan, suke taimakawa mutane ko da kuwa Musulmai ne ko ba Musulmai ba.

Ya kara da cewa tarbar da ya samu a Jeddah da kuma dangantakar aikin shi da Qur’ani ya sanya ya karbi Musulunci.

“Larabawa na bautawa Allah guda daya kawai, kuma suna da kyawawan dabi’u,” in ji shi.

Shropshire wanda yake zaune a kasar Saudiyya yanzu, ya kafa wata kungiya ta kawo zaman lafiya da sulhu.

Bayan haka kuma ya zama shugaban al’umma tare da gudanar da kungiyoyin masu zaman kansu daban-daban don daukaka Musulunci da Musulmai.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here