Allahu Akbar: Farfesan kasar Faransa ya Musulunta bayan yayi bincike akan gawar Fir’auna mai shekaru 3,000

0
1166

Maurice Bucaille dan asalin kasar Faransa ne, kuma yana bin addinin Kiristanci kamar yadda iyayenshi suka koya mishi. Bayan kammala makarantar sakandare, ya cigaba da karatu a fannin likitanci a jami’ar kasar Faransa.

Daga baya Maurice ya zama likita mafi wayo da iya aiki a kasar Faransa, amma wani abu ya faru da ya canja masa rayuwa baki daya.

Kowa dai ya san kasar Faransa wajen binciken abubuwan tarihi. A lokacin da tsohon shugaban kasar Faransa Francois Mitterrand ya hau mulki a shekarar 1981, kasar Faransa ta bukaci kasar Misra da ta bata gawar Fir’auna domin ta gabatar da bincike a kanshi.

A lokacin aka kai gawar Fir’auna kasar ta Faransa, cikin abin mamaki sai shugaban kasar Faransa na lokacin da ministocinsa da sauran manyan kasar suka jeru a layi suka duka a gaban jirgin da yake dauke da gawar ta Fir’auna kamar dai yana raye.

Bayan kai gawar kasar ta Faransa, Farfesa Maurice Bucaille, aka bawa damar shugabantar bincike akan gawar ta, a lokacin da masu binciken suke ta faman aiki, ashe basu sani ba shugabansu yana can yana wani tunani na daban.

A lokacin yana ta tunanin yadda aka yi Fir’auna ya mutu, a ranar da ya kammala binciken shi ya gano cewa ya mutu a ruwa ne, amma abinda ya tsaya a ranshi shine ya aka yi duk tsawon wannan lokacin gawarshi ba ta rube ba duk kuwa da cewa a cikin ruwa aka dauko gawarshi.

Ya cigaba da mamaki, kuma ya cigaba da tambaya, “Shin ya aka yi Qur’ani ya bayyana wannan abin mamaki, bayan ba a samo gawarshi ba sai a shekarar 1898, shekaru 200 da suka wuce, inda shi kuma Qur’ani an aiko dashi ga Musulmai shekaru 1400 da suka wuce, haka kuma shekarun da suka wuce duk duniya babu wanda yasan da cewa an ajiye gawar Fir’auna.

Maurice Bucaille ya kwashe kwanaki yana ta faman bincike akan gawar Fir’auna, sannan kuma ya cigaba da tunani akan maganar da abokanan aikinshi suka gaya masa dangane da gawar da kuma abinda Qur’ani yace a kanta, inda shi kuma Bible yayi magana akan yadda Fir’auna ya dinga bin Annabi Musa ne ba tare da bayyana abinda ya faru da gawarshi ba.

“Shin da gaske ne Annabi Muhammad (SAW) ya san da labarin Fir’auna shekaru 1,000 da suka wuce inda ni kuma sai yanzu nake sani?” ya ce. Maurice ya kara shafe wasu kwanakin a haka, a karshe ya bukaci a bashi littafin At-Taura mai fassara, amma ita ba ta yi magana akan yadda gawar Fir’auna ta nutse a ruwa ba.

Bayan an mayar da gawar kasar Misra, Maurice ya tattara kayansa ya nufi kasar Saudiyya, inda yayi magana aka gawar ta Fir’auna. A wajen taron da ya halarta a kasar ta Saudiyya wani daga cikin mahalarta taron ya bude Qur’ani ya karanto masa ayar da tayi magana akan Fir’auna, inda Allah ya ce:

“A yau zamu mayar da kai da gawarka, domin ka zama aya ga wadanda suke gabaninka. Kuma lalle ne masu yawa daga mutane, haƙiƙa, gafalallu ne ga ayoyinmu. (Yunus: 92)

Cikin mamakinshi, sai ya tashi tsaye a wajen taron ya ce: “Na Musulunta kuma na yadda da wannan Littafi mai suna Qur’ani.”

1 COMMENT

  1. Assalamu Alaikum Allah ya saka DA Alkhairi hakika na ailmnatu DA wannan rubutu naku kuma na qara imani sosai Allah yayu muku jagora ya qara ilimi DA daukaka.

    Na godw

  2. Assalamu Alaikum Allah ya saka DA Alkhairi hakika na ailmnatu DA wannan rubutu naku kuma na qara imani sosai Allah yayu muku jagora ya qara ilimi DA daukaka.

    Na godw

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here