Allahu Akbar: Farfesa kasar Turkiyya ya rasu da azumi a bakinshi, rungume da Al-Qur’ani mai girma

0
313

Kowa yaji wannan maganar da ake cewa, kowa na mutuwa yadda yake rayuwa. Wannan ya zama gaskiya a yayin da Farfesan da ya kware wajen karatun Al-Qur’ani ya koma ga Allah a yayin da yake karanta littafin mai girma a kasar Turkiyya.

Ustadh Mehmet Ali Shaflak, Malami ne na Al-Qur’ani mai girma kuma Farfesa ne wanda ya kari rayuwarshi wajen karanta Al-Qur’ani mai girma. Ya kare rayuwarshi wajen kokarin koyar da Al-Qur’ani mai girma, haka kuwa Allah ya karbi ranshi a lokacin da yake karanta littafin mai girma.

Allah ya karbi rayuwar Ustadh Shaflak a ranar da aka dauki azumi na biyar, wato ranar 28 ga watan Afrilu, inda ya rasu yana da shekara 94.

Kamar yadda muka ji a wasu Fatawoyi da yawa, idan mutum ya rasu a watan Ramadana, Allah yana gafarta masa zunubansa cikin ikon Allah.

Allah ya yiwa Ustadh Shaflak rahama ya saka masa da Aljannah Firdaus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here