Allahu Akbar: Bayan sati biyu da aurensu, minti biyar kafin rasuwarsa Amarya ta yiwa Angonta bidiyo na karshe

0
211

Wani labari mai daukar hankali da sa dan adam jimami da tunanin duniya ba abakin komai take ba ya faru a garin Kano, inda wani ango yayi mutuwar ba zata bayan sati biyu da auresu.

Ba mutuwar sa a mako biyu da aurensu ne yafi bawa mutane tu’ajjibi ba illa yadda cikin mintuna biyar kafin rasuwar sa amaryar sa tayi masa bidiyo, inda a cikin bidiyon anji shi yana cewa shi fa kansa ne ke masa ciwo, inda kamar yadda amaryar ta bayyana, ba a fi minti biyar da hakan ba ya yanke jiki ya fadi Allah ya amshi rayuwarsa.

Wannan al’amari ya daga hankalin al’umma matuka, ya kuma karawa masu imani tsoron Allah da hakikancewa duniya gidan aro ce ran dan adam ba a bakin komai yake ba, a kowanne lokaci zai iya zama sa’inka na karshe.

Allah ubangiji ya jikanshi ya yi masa Rahama, muma idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da imani. Amin.

Ga dai bidiyon wanda tashar YouTube ta Tsakar Gida ta wallafa a shafinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here