Allahu Akbar: Bayahude ya Musulunta bayan ya ga Manzon Allah (SAW) a cikin mafarki

0
354

Wani Bayahude mai suna Sanford Pass, ya Musulunta, inda yake bayar da labarin yadda lamarin ya faru da shi.

Sanford ya bayyana yadda aka yi ya Musulunta a wani shirin talabijin mai suna ‘TheDeenShow’, inda aka yi hira da shi akan dalilin da yasa ya shiga Musulunci.

Da aka tambayi Sanford akan abinda yasa ya shiga Musulunci ya ce shi bai san komai ba dangane da addinin Musulunci. Bai taba haduwa da wani mutum Musulmi ba. Amma akwai wata rana da yayi mafarki wanda ya canja masa rayuwa baki daya.

Sanford ya ce yaga mutum a cikin mafarkin na shi amma bai iya ganin ainahin fuskarshi ba, amma ya ce ya tabbata mutumin yana kallon shi ne yana murmushi.

Ya ce gari na wayewa yaje ya samu wani Limamin masallaci ya bayyana masa mafarkinsa, Malamin ya ce masa manzon Allah ne (SAW) ya kai masa ziyara a cikin mafarkinsa. Sanford ya ce yaga mutumin cikin kaya farare da rawani a kansa mai kyalli kamar gwal.

Ya ce inda yake a tsaye haske ya cika wurin bai iya ganin fuskarshi ba. Ya ce tun daga wannan lokacin yaji sanyi a cikin zuciyarsa, kuma yaji farin ciki. Ya kara da cewa bayan ya sanar da mutane mafarkinsa da yawa suna cewa yayi mafarkine na musamman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here