Allahu Akbar: Baturiya ta Musulunta bayan ta auri Musulmi bakar fata

0
432

Idan Musulunci ya shiga zuciyar mutane yana canja musu rayuwa ne baki daya. A kusan kowacce rana muna karanta labari game da Musuluntar mutane a shafukan sadarwa.

Wannan labari na yau yana da matukar ban sha’awa, inda wata Baturiya ta auri wani saurayi dan kasar Gambia a kasar Jamus, bayan tayi watsi da wariyar launin fata, sannan ta tabbatar da cewa Musulunci babu ruwanshi da kalar fata ko yankin da mutum ya fito daga.

Baturiyar ba wai iya auren shi kawai tayi ba, ta Musulunta ne kuma aka fara azumin watan Ramadana da ita.

Budurwar ‘yar kasar Jamus ta Musulunta bayan ta auri saurayin ta kuma canja sunanta zuwa Fatima.

“Na Musulunta shekarar da ta gabata, mijina bai tilasta ni sai na karbi addininshi ba, ni na yanke shawarar shigowa Musulunci da kaina. Ina so na daina zuwa coci,” ta ce. Fatima ta kara da cewa: “Ina azumi, wannan shine azumin farko da nayi.”

A cewarta, tana jin dadi sosai bayan shigowarta Musulunci, sannan mijinta da suka yi aure shekara biyu da suka wuce yana matukar alfahari da ita da ta dawo addinin Musulunci.

“Ina fatan ni da mijina zamu je kasar Gambia kafin karshen shekarar nan domin na hadu da ‘yan uwanshi da abokanan shi a karon farko. Annobar Coronavirus ta sa komai ya canja a duniya,” cewar Fatima wacce ke zaune a birnin Osnabruck arewa maso yammacin kasar Jamus ita da mijinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here