Allahu Akbar: Bature da ya ziyarci kowacce kasa dake duniya ya karbi addinin Musulunci a karshe

0
1521

Musulunci wuri ne na duk wani mutumi da yake neman gaskiya. Imani na shiga zuciyar mutum idan Allah ya so hakan. Saboda haka Allah ne kadai yake da iko akan shiryar da wanda ya so.

Wannan labarin wani mutumi ne da ya tsinci kanshi a hali na neman gane wane ne ubangiji na gaskiya. Ya ziyarci kowacce kasa ta duniya a lokacin da yake da shekaru 27 a duniya, inda a karshe ya karbi addinin Musulunci.

Mutumin mai suna Sal Lavallo, an haife shi a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 1990, shekaru 11 kafin harin benayen Amurka na 9/11. Ya zama matashi na farko da ya fara ziyartar kowacce kasa a duniya yana dan shekara 27.

Ya shiga makarantar Katolika inda ya shafe shekaru 11. Sai dai a lokuta da dama iyayenshi na gaya masa cewa ana samo imani a waje ne, saboda haka ba komai bane dan ya samu wani ilimi daban da wanda aka koya masa a coci.

A lokacin da yake dan shekara 17, Sal ya fara ganin annabi Isah (AS) a matsayin manzon Allah ba wai a matsayin ubangiji ba. A lokacin ya kasa samun nutsuwa ko kadan a zuciyarsa akan gaskiyar wanene Allah.

Duka wannan ya faru a lokacin da yake ziyartar gabashin Afrika, kasar Saudiyya, Inda, Nepal da kuma Venezuela. Wannan tafiye-tafiye da ya fara yi yasa ya fara gano gaskiyar addinai.

A shekarar 2013, a wani kauye dake kasar Tanzania, ya hadu da wani mutumi wanda ya tambayeshi game da abinda yayi imani. Sal ya sanar da mutumin akan halin da yake ciki na neman ilimi akan wanene Allah. Bayan ya kammala bashi labarin mutumin ya kira shi da Musulmi.

Ai kuwa sai ya fara bincike akan Musulunci ya kuma dinga samun abinda zuciyarshi take bukata daya bayan dayan. Ya samu ilimi sosai na Musulunci, ya koyi yanda ake sallah, ya san duka annabawan Allah. Sal ya karbi kalmar Shahadah a wannan rana.

Washe gari ya maimaita kalmar Shahadah a cikin jama’a a wajen wani limami. Bayan cigaba da bincike akan Musulunci, a hankali sai ya gano inda gaskiyar take, inda ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da yaji a zuciyarshi cewa yana kan gaskiya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here