Allahu Akbar: Babban Malamin addinin Musulunci Allama Khalid Mahmood ya koma ga Allah a cikin wannan wata mai alfarma

0
205

Babban Malamin addinin Musulunci, Allama Khalid Mahmood ya koma ga Allah a cikin wannan wata mai daraja, ya rasu a yau 14 ga watan Mayu. Babban Malamin Sunna ne a kasar Pakistan, kuma shine marubucin littafin ‘Aasaar-ut-Tanzeel’.

Malamin yayi kaurin suna sosai a duniya, Har yanzu ba a bayyana ainahin yadda mutuwar tasa ta kasance ba. Allama ya rike mukamin alkalin alkalai na kotun kolin kasar Pakistan, haka kuma ya rike mukamin daraktan na makarantar addinin Musulunci dake Machester kasar Birtaniya. Ya rike mukamai da yawa na kungiyoyi da cibiyoyin bincike na ilimi.

Allama yayi karatun ilimi akan addinai da dama. An bayyana shi a matsayin malamin da yafi kowa samun alfarma a duniya. Mutuwarshi a cikin wannan wata na Ramadana mai alfarma ya sanya mutane ke ta faman yi masa zaton dacewa da gidan Aljannah.

Allah yayi masa albarka ya kuma jikansa da Rahama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here