Allahu Akbar: Babban daraktan Hollywood ya yabi Suratul Fatiha ya kuma kare addinin Musulunci

0
768

Daya daga cikin manyan daraktocin kamfanin fina-finai na Hollywood, Francis Ford Coppola, ya yabi addinin Musulunci ya kuma yi bayanin Suratul Fatiha ta hanyar da ta dace a wajen wani taron fim da aka gabatar na Marrakech International Film Festival.

Daraktan dan asalin kasar Italiya da yake zaune a kasar Amurka yayi magana akan Suratul Fatiha sannan kuma ya kara jadadda kalmar zaman lafiya, yafiya, da kuma soyayyar juna da Al-Qur’ani mia girma yake koyar da mutane.

Coppola na amsa tambaya ne a wajen taron inda ya kawo Suratul Fatiha a ciki. “Idan har kun san Qur’ani, kalma ta farko a ciki ita ce: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Godiya ta tabbata ga Allah, ubangijin halittu, mai rahama mai jin kai,’ inji Coppola.

Coppola lokacin da yake bayani a wajen taron Bidiyo: YouTube

‘Duk wanda ya san da wannan addini, wanda ya koyar da wayewar kai tun a karni na 13, ya san cewa tushen wannan addini, kamomi ne guda biyu masu muhimmanci sune Allah mai Rahama, Allah mai jin kai, kuma mun dogara ga Allah ya fito damu daga cikin wannan kangi da ake da mutane ke wahala,” ya kara da cewa.

Yadda yayi bayani akan ayar Qur’anin ya kuma kare Musulunci ya sanya idon mutane da yawa zubar da kwalla. Mutanen da suka je wannan wajen taro duk sun tashi jikinsu babu karfi.

Ga wadanda basu san wanene Francis Ford Cappola ba; shine daya daga cikin manyan daraktoci na kamfanin Hollywood.

An haife shi a Detroit, Michigan, mahaifinshi dan kasar Amurka ne mai suna Carmine Coppola, inda mahaifiyarshi kuma take ‘yar kasar Italiya mai suna Nee Pennio. Babban fim din shi da yayi suna shine ‘Godfather I, II, & III’, banda su kuma Cappola yayi fina-finai masu yawan gaske da suka yi suna.

Yana daya daga cikin mutane shida a duniya da suka taba karbar lambar girma ta Oscar saboda kwarewa a iya aikin fim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here