Allahu Akbar: Amarya ta koma ga Allah a cikin daren da aka daura mata aure

0
1004

Wata kyakkyawar amarya ‘yar kasar Egypt mai suna Jihar Omar Hamad ta koma ga Allah a cikin daren da aka daura mata aure a birnin Al-Menia.

A lokacin, Jihad wacce ke da shekaru 22 a duniya tana murnar daya daga cikin raneku mafi farin ciki a rayuwarta, kawai sai gani aka yi ta suma.

Anyi gaggawar garzayawa da ita zuwa asibiti, amma likitoci sun bayyana cewa ta mutu bayan wani dan lokaci. Duk da dai cewa basu bayar da dalilin da ya saka ta mutu ba, amma ana kyautata zaton bugun zuciya ta samu.

Ta samu bugun zuciyar ne dai jim kadan bayan an kammala biki kowa ya wuce amarya da ango sun tare a cikin sabon gidansu za su fara rayuwar aure.

Mutuwar Jihad ya sanya angonta, ‘yan uwa da abokanan arziki cikin tashin hankali. Haka kuma labarin nata ya sanya mutane da yawa jimami bayan ya fara yawo a shafukan sadarwa.

A wani rahoto makamancin haka kuma Press Lives ta kawo muku rahoton bikin shugaban hukumar kwastam na Najeriya Kanal Hamid Ali da sabuwar amaryar da ya aura a jihar Kano.

Tsohon gwamnan jihar Kadunan na mulkin soja ya sake sabon auren ne bayan mutuwar tsohuwar matarsa da shekara biyu. Ga dai wasu daga cikin hotunan angon da amaryarsa.

Hotuna: Shugaban hukumar kwastam na kasa Kanal Hamid Ali ya angwance da zankadediyar budurwa a jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here