Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un, dama dai an ce daga Allah muke kuma gareshi zamu koma koda ciwo ko babu ciwo, yanzu muke samun rasuwar wani bawan Allah a garin Maiduguri dake jihar Borno.
Mutumin ya Allah ya karbi ranshi a yau Lahadin nan 24 ga watan Mayu, 2020, a tsakiyar filin idi.

Ya rasu a filin idi na Polo dake garin Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda har ya zuwa yanzu da muka kawo rahoton ba a bayyana ainahin abinda ya kashe shi ba.
Muna rokon Allah ya jikanshi ya sa ya huta, muma idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da imani.
A yau ne dai ake gabatar da bikin karamar sallah a fadin Najeriya da wasu kasashe na duniya, yayin da cutar Coronavirus ta sanya sallar a wannan karon ta zama daban.