Allahu Akbar: Allah ya dawo da rayuwar wani jariri da aka binne da rai a cikin kabari

0
1297

Wani bidiyo mai ban al’ajabi na ta yawo a shafukan sadarwa. Da yake nuna yadda wani mutumi yake hako wani kabari domin ceto rayuwar wani jariri, abin mamaki kuma shine Allah ya basu ikon ceto rayuwar yaron.

Wani jariri sabuwar haihuwa da aka binne da ranshi ‘yan kauyensu sun samu nasarar ceto rayuwarshi. Jaririn wanda aka gano kafarsa ta leko daga cikin kabarin bayan mutanen dake ginin gida a kusa da wajen sun jiyo kukan shi suka fara neman inda yake.

An samo shi cikin ramin a kauyen Sonoura dake arewacin Uttar Pradesh dake kasar Indiya. Mutanen kauyen sun bude ramin inda suka zaro yaron daga ciki. Cikin gaggawa aka garzaya dashi asibiti.

Likitocin sun bayyana cewa jaririn ya hadiye kasa da yawa wacce ta rufe masa hanyar numfashinsa, amma daga baya jaririn ya sami lafiya. Wani daga cikin mazauna kauyen ya nemi a bashi ya cigaba da rikon yaron, wanda likitocin ke cigaba da kula da shi a lokacin.

Ya zuwa yanzu dai tuni ‘yan sanda sun fara bincike akan lamarin, inda ake neman wani mutumi da ake tunanin yana da hannu a lamarin.

Idan ba a manta ba Press Lives ta kawo muku wani rahoto makamancin haka da ya nuna yadda wasu ‘yan sanda suka ceto rayuwar wata jaririya da suka tsinta a cikin bola a jihar Neja.

Jaririyar dai an garzaya da ita asibiti, inda likitoci suka yi kokarin ceto rayuwarta, cikin ikon Allah kuma aka dace, inda har likitan da ya wallafa labarin ya nuna sha’awarsa akan cigaba da kula da yarinyar.

Ana ta cigaba da samun abubuwa makamanta da wannan dai yayin da kuma lamari na zubar da ciki yake kara kamari a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here