Allah yasa muyi kyakkyawan karshe: Karuwa ta jefo kwastoma daga kan bene tsirara haihuwar uwarshi (Bidiyo)

0
244
  • Karuwa ta kashe wani mutumi da yaje yin lalata da ita kasar Ghana ta hanyar tunkudo shi daga kan bene
  • An bayyana cewa mutumin ya fado daga kan benen tsirara haihuwar uwarshi da kwaroron roba a gabanshi
  • Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mutumin yayi barazanar kashe karuwar ne a lokacin da yake lalata da ita

Ofishin hukumar ‘yan sanda na Asokwa dake kasar Ghana sun kama karuwai 11, bayan daya daga cikinsu ta turo wani mutumi daga kan bene a otel dake Kumasi.

Lamarin dai ya faru a ranar Lahadi ne, 10 ga watan Mayun shekarar 2020, a otel din Anidaso dake Kumasi yankin Ashanti.

Mutumin dai an bayyana yana tsakanin shekaru 30 ne a duniya, an bayyana cewa an turo shi daga tagar otel din ne a lokacin da yaje yana lalata da daya daga cikin karuwan.

Wani da lamarin ya faru a gabanshi ya ce mutumin ya fado tsirara ne da kwaroron roba a gabanshi, inda ya mutu a take a wajen.

Mutanen cikin otel din sun bayyana cewa sun jiyo hayaniya a cikin otel din, amma sunyi tunanin daya-biyu ne da mutanen otel din suka saba yi, sai daga baya suka ji cewa ai wani ya mutu.

Bayan an gabatar da bincike, ‘yan sanda sun bayyana cewa mutumin wanda yake bako ne a otel din yayi barazanar kashe karuwar.

Da yake magana da Joy News, jami’in dan sanda Christoper Owusu Mpianin, ya tabbatar da cewa ‘yan sanda suna kan cigaba da bincike akan lamarin domin gano yadda aka yi mutumin ya mutu.

A karshe dai an kai gawar mutumin zuwa asibiti domin cigaba da bincike a kai.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya faru a kasa:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here