Allah Sarki: Tsananin yunwa ta sanya ta fara dafa duwatsu domin ta kwantar da hankalin ‘ya’yanta su dauka abinci ne

0
350

Wata mata mai ‘ya’ya guda 8 ta koma dafa duwatsu domin hankalin ‘ya’yanta ya kwanta su dauka cewa abinci take dafa musu.

Matar mai suna Peninah Bahti Kitsao, bazawara ce dake zaune a birnin Mombasa na kasar Kenya, tana aikin wanki ne kafin a sanya dokar hana fita.

Sanadiyyar annobar Coronavirus yasa komai nata ya ja baya ya zama mutanen dake kawo mata wanki sun daina, kuma ta daina samun kudi.

A ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, bayan ‘ya’yanta sun addabeta da kuka ta tarkato duwatsu ta fara dafa musu domin ta samu ta kwantar da hankalinsu su dauka cewa abinci ne take dafa musu. Inda ta dinga addu’ar Allah yasa bacci ya dauke su a lokacin da suke jiran abincin.

Sai dai kuma ‘ya’yanta basu iya bacci ba saboda yunwa, inda har makwabciyarsu da kukan yaran ya dameta ta shiga gidan taga halin da suke ciki.

A cewar matar mai suna Prisca Nyakaragio Momanyi, taji yaran suna ta kuka sai ta garzaya gidan domin taga abinda ke faruwa, kawai sai ta iske mahaifiyarsu tana dafa musu duwatsu.

Prisca ta baiwa sauran makwabtansu labari, sai kuma aka fara sanya labarin a kafafen sadarwa.

Gidan talabijin na Kenya NTV ya gana da matar, inda mutane da yawa suka dinga kai mata kayan taimako.

Matar ta ce ba ta taba tunanin cewa mutane zasu kawo mata dauki ba, inda ta bayyana cewa ta tabbata mu’ujiza ce ta ubangiji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here