Allah Sarki: Bidiyon yadda aka ceto rayuwar wani jaririn yaro da ya fada rijiya mai ruwa

0
118

Wani jariri da ya fada cikin wata rijiya ya rayu bayan wasu samari sun sayar da rayuwarsu sun ceto shi.

A wani bidiyo da aka dauka a jihar Anambra, ya nuna tarin mutane sun zagaye rijiyar, inda suke ta nuna jimami akan yaron da ya fada cikin rijiyar.

Wani jarumin saurayi yayi kukan kura ya fada rijiyar, inda ya daura igiya a jikin jaririn wadanda suke waje suka jawo yaron a hankali, inda aka dace yaron ya fito da rai kuma cikin koshin lafiya.

Jarumin da ya shiga cikin rijiyar daga baya ya fito ya bayyanawa mutanen cewa rijiyar na da matukar zurfi.

Anyi ta yi masa godiya akan namijin kokarin da yayi, inda aka dauki jaririn aka kwantar dashi akan tabarma domin ya huta.

Wasu sunyi tunanin yaron ya sha ruwa da yawa, inda suka dinga danna cikin yaron, domin fito da ruwan, amma daga baya sun gane cewa yaron lafiyar shi kalau.

Ga dai bidiyon a kasa:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here