Allah Sarki: Bai san hawa ba bai san sauka ba, an kashe maigadi da duka saboda an sace waya a Bauchi

0
323

Wasu mutane da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kashe wani saurayi mai suna Sunday Ezra a New Trafford Hotel dake Gwallameji cikin jihar Bauchi.

Lamarin ya faru da yammacin ranar Litinin, a lokacin da mutanen yankin suka yi masa dukan tsiya har sai da ya zama baya iya motsi suka gudu, inda ya mutu a lokacin da ake shirin kai shi asibiti.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa an kashe shi ne bayan an sace wata waya mai tsada a cikin otel din, kuma yana daga cikin wadanda ake zargin sun saci wayar, inda shi kuma ya musanta wannan zargi da ake yi masa.

Majiyar ta ce mutanen da suka taru akan wayar basu yadda da maganar shi ba, kawai sai suka fara dukansa da niyyar ya fada musu gaskiya, amma bai ce musu komai ba.

A yayin da suke dukan shi ne jini ya dauke shi ya fadi kasa, inda suka yi gaggawar daukar shi zuwa ofishin ‘yan sanda a cikin Keke Napep, a lokacin da ake shirin kai shi asibiti kuma ya mutu a hanya.

Sai dai kuma daga baya an ruwaito cewa an samu wayar a hannun wani wanda aka ce ya dauke ta ne a wajen da mai wayar ya jefar bai sani ba.

Jami’an hukumar ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an kai rahoton lamarin ofishinsu dake Yelwa, inda su kuma yanzu suke kan bincike domin gano gaskiyar lamarin.

‘Yan sandan sun ce duk da dai an kama wasu daga cikin wadanda keda hannu a kisan, har yanzu suna cigaba da iya bakin kokarinsu wajen kamo sauran, inda da zarar sun kammala kama su za su aika su gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here