Allah ne yake jarraba imanin mu da annobar coronavirus – Atiku Abubakar

0
214

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce annobar coronavirus a Najeriya jarrabawa ce daga Allah.

Ya ce a Musulunci, Musulmai sun yadda cewa babu wani abu da zai faru ba tare da izinin Allah ba.

A sakon da ya aika na sallah a jiya Asabar, Atiku ya bukaci ‘yan Najeriya da su cigaba da bin dokar da hukumomin lafiya suka gindaya.

Ya ce: “Duka wadannan dokokin baza su saka Allah yaki karbar azumin mu ba, saboda a matsayinmu na Musulmai mun yarda cewa komai yana faruwa da izinin Allah ne. Mun ilimantu a Qur’ani da sunnar manzo cewa Allah yana jarabtar mu ta kowacce hanya.

“Halin da muke ciki a yanzu na annobar Coronavirus jarrabawa ce daga Allah, munyi azumi dukan mu a matsayinmu na Musulmai, dan haka mu cigaba da tunawa cewa yana daya daga cikin cikar imaninmu mu kare lafiyar mu sannan mu bi dokar da hukuma ta sanya a kanmu, musamman a lokaci irin wannan.

“Wannan dokoki na hana taron jama’a, hana kusantar juna da kuma yawan wanke hannaye duka an sanya su saboda lafiyar mu ne dama duka rayukan al’ummar duniya baki daya.

“A matsayinmu na Musulmai yana da matukar muhimmanci muyi iya bakin kokarinmu wajen ganin duniya ta warke daga wannan cuta mai kisa.

Haka kuma Atiku ya shawarci gwamnati da ta tabbatar da jin dadin da kare lafiyar al’umma a wannan lokaci na coronavirus.

Ya ce: “Duka shugabannin duniya suyi koyi da halayen fiyayyen halitta Annabi Muhamad (SAW) da sahabbansa, wajen tafiyar da mulkinsu da kuma lura da lafiyar al’umma.

“Wannan lokaci ne da shugabanni za su sayar da rayukansu, ba lokaci bane na rayuwa ta almubazzaranci ba. Bikin sallah na wannan shekarar kowa ya san daban ne.

“Saboda haka ina yiwa mutanen Najeriya dama al’ummar duniya baki daya barka da sallah.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here