Allah ne kadai zai sakawa Abacha akan irin kokarin da ya yiwa Najeriya – Hamza Al-Mustapha

0
2054

Hamza Al-Mustapha, babban dogarin tsohon shugaban kasar mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana cewa Allah ne kadai zai iya sakawa tsohon ubangidan nashi akan irin kokarin da ya yiwa Najeriya kafin ya mutu a ranar 8 ga watan Yunin shekarar 1998.

Da yake jawabi a wajen bikin tunawa da shi na 22 da aka gabatar a jihar Kano ranar Litinin 8 ga watan Yuni, Al-Mustapha ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar yayi aiki tukuru akan tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata a Najeriya. Ya ce kafin mutuwar tsohon shugaban kasar akwai sama da dala biliyan tara a cikin asusun kasashen waje na Najeriya.

Ya kara da cewa a lokacin tsohon shugaban kasar duka dala 1 ana sayar da ita akan naira 85 ne, ya kara da cewar babu wani hauhawar farashi duk da matsaloli da kalubalen da ke gaban gwamnati a wancan lokacin.

“Abinda Abacha ya yiwa Najeriya ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin Najeriya.

‘A lokacin da Abacha ya hau mulki dala miliyan 200 ne kawai a cikin asusun kasashen waje na Najeriya, kafin ya rasu ya samu damar farfado da tattalin arzikin ya daidaita shi har sai da kudin dake asusun kasashen wajen na Najeriya ya kai dala biliyan 9.

“Allah ne kawai zai sakawa Janar Sani Abacha akan irin kokari da yayi na ganin ya canja Najeriya ta samu cigaba,” ya ce.

Mutane na tuna Abacha ne akan kudin da ya boye a kasashen ketare.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here