Allah mun tuba: Bakuwar cuta mai kama da Coronavirus ta fara halaka kananan yara a Turai

0
245

Gwamnan New York dake kasar Amurka, Andrew Cuomo, ya bayyana mutuwar wani yaro karami mai shekara biyar a duniya, bayan ya sha fama da wata irin cuta da ta sanya masa kumburi a gefen zuciyarsa, wacce masana a fannin kimiyya suka bayyana cewa tana da alaka da cutar coronavirus.

Andrew ya bayyana cewa ranar Alhamis yaron ya mutu, sannan ya kara da cewa ya zuwa yanzu akwai wasu yaran guda 73 da suka kamu da cutar.

A karshen watan Afrilun da ya gabata ne dai hukumomin lafiya na kasar Birtaniya da Faransa suka fara bayyana bullar cutar wacce ke damun kananan yara da masana suka danganta ta da cutar Coronavirus.

A cikin watan Afrilun ne kuma hukumomin lafiya na kasar ta Birtaniya da Faransa suka bayyana cewa an kwantar da yara masu yawa a asibitoci sanadiyyar kamuwa da sabuwar cutar, wacce ya zuwa yanzu dai ba a saka mata suna ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here