Allah mai yadda yaso: Mata da miji sun Musulunta bayan sun kalli fim din ‘Diriliş: Ertuğrul’ wanda Zakir Naik yace haramun ne Musulmai su kalla

0
248

Diriliş: Ertuğrul fim ne mai dogon zango da yayi suna matuka a duniya, wanda ya karya alkadarin duka wasu fina-finai na kasar Turkiyya.

Wannan fim dai yana nuni game da rayuwar Ertugrul Gazi, mahaifin Osman Ghazi, wanda ya samar da Babbar Daular Ottoman, wato Great Ottoman Empire a turance.

Wannan daula dai a wancan lokacin ta Musulmai ce da ta hada da yankin Asiya da kuma yankin Turai. Fim din yana nuni akan karfin wannan bawan Allah Musulmi wanda yake matukar kaunar Allah da manzonsa da kuma addinin Musulunci.

Sunan wannan fim ya jawo hankalin miliyoyin mutane daga kowanne lungu da sako na duniya wajen kallon shi.

Abubuwan da aka sanya a cikin wannan fim ya sanya wasu ma’aurata ‘yan kasar Mexico suka karbi addinin Musulunci.

Zancen gaskiya wannan fim ya sanya nutsuwa a cikin zuciyar Musulmai wadanda suke fama da wasi-wasi a zuciyarsu. Wannan fim ya nuna musu yadda magabatansu suke.

Ma’auratan sun Musulunta shekarar da ta gabata, bayan sun hadu da Celal Al wanda ya fito a matsayin Abdurrahman Alp a cikin fim din. Ma’auratan sun karanta kalmar Shahada a gaban Celal a lokacin da ya kai ziyara kasar Amurka.

Ma’auratan ba wai sun karbi Musulunci bayan kammala kallon fim din bane, a’a sun gabatar da bincike mai zurfi kafin suka gano gaskiya game da addinin Musulunci wanda turawan yamma suka batawa suna.

Celal ya bawa ma’auratan kyautar Qur’ani guda biyu daya da aka fassara da Turanci, daya kuma da yaren Sipaniya.

Bayan karbar addinin Musulunci, mata da mijin sun ce: “Fim din Diriliş: Ertuğrul ya taba mana zuciya, kuma irin ayyukan jin kai da kasar Turkey take yi a duniya ya sanya muka yanke hukuncin Musulunta.

Wannan fim dai ya jawo hankalin Musulmai masu yawan gaske, inda yake nuni akan Musulmai na gaskiya, sai dai kuma ya samu kalubale.

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan na duniya Dr Zakir Naik ya bayyana wannan fim a matsayin haram kuma ya bukaci Musulmai da kada su kalli wannan fim.

Sai dai duk da haka, wannan fim dai ya zama zakaran gwajin dafi, domin kuwa duk da shekara hudu bayan fitowarshi har yanzu yana nan yana ta yawo a kasuwa, kuma mutane na ta faman kallon shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here