Allah mai iko: Bakar fata da aka sayar da ita a matsayin baiwa ta zama daya daga cikin masu kudin kasar Amurka

0
2425

Labarin Princess Anta Madjiguene Ndiaye yana daya daga cikin labaran da yake bawa mutane mamaki idan suka karanta. Matar wacce take ‘yar asalin kasar Senegal, an kamata an sayar da ita a matsayin baiwa.

‘Yan uwanta sai da suka shafe sama da karni biyu basu san inda take ba. A shekarar 2018 sun samu daddadan labari.

An sayar da Princess Anta a shekarar 1806 a masarautar Wolof. ‘Yan uwanta sun hakura da ita, bayan shafe shekaru suna nemanta babu amo babu labari.

Bayan an fitar da rai da ita, an gabatar da jana’izarta, an gabatar da duka bukunkuna koda ace ma kasheta aka yi.

Bayan an kamata, an kai ta tsibirin Goree tare da wasu bayi, har zuwa lokacin da aka fito dasu aka fara tallata su a kasuwa.

An sayar da Princess Anta, inda aka kai ta kasar Cuba. A Cuba, an kara sayar da ita zuwa kasar Amurka ga Zephaniah Kingsley, wanda yake da wata babbar gona.

Kingsley ya fara sonta, inda har ta kai ga sunyi aure, suka haifi yara hudu. Bayan sunyi aure aka canja mata suna zuwa Anna Kingsley.

Duk da a wancan lokacin dokar kasar Amurka bata bari Bature ya auri bawa ba, sunyi aurensu a Cuba kafin Kingsley ya bata ‘yanci.

A cikin shekara biyar kawai ta zama baiwar da tafi kowa kudi, bayan Kingsley ya bata iko akan dukiyarshi.

Bayan an sayar da Florida, sun koma Cuba da zama a lokacin da aka bayyana cewa aurensu ya saba doka. A kasar Cuba suka fara noma, tare da cigaba da lura da ‘ya’yansu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here