Aljanu ne suka shiga jikina: Cewar magidanci da ya yiwa ‘yarshi mai shekaru 3 fyade a yayin da matarsa ke nakuda

0
2596

Wani magidanci mai shekara 43 ya shiga hannun hukumar ‘yan sanda bayan an kama shi da laifin yiwa ‘yarshi mai shekaru 3 fyade, a yayin da matarsa ke asibiti tana nakuda za ta haifa masa jariri.

Mutumin mai suna Mr Ikechukwu Ekenta daga Ikeduru-Ogwah karamar hukumar Mbaitolu cikin jihar Imo, ana zargin shi da yiwa ‘yarshi mai suna Kamsiyochukwu Ekenta, fyade a ranar 28 ga watan Afrilu, 2020, a lokacin da mahaifiyarta ke asibiti.

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, yarinyar mai shekaru uku da watanni 10, ta ce mahaifin nata ya saka gabansa a nata a lokacin da take bacci, ta ce zafin abin ne ya tashe ta daga bacci.

Da yake magana a cibiyar cigaban mata ta Farfesa Dora Akunyili dake Akwa, mutumin da ake zargin, ya ce shaidan ne ya yaudare shi har ya aikata wannan mummunan aiki.

Ya ce a duk lokacin da aljanun suka shiga jikinshi, sai ya fara yin wasu abubuwa marasa kan gado, ya ce a wannan ranar yayi amfani da hannunsa ne yayi lalata da ‘yar tashi.

A lokacin da matar mutumin mai suna Mrs Uzoamaka Ekenta, take bayani akan yadda taji lamarin bayan dawowarta gida daga asibiti, ta ce ta tarar da ‘yarta tana yin wasu abubuwa kamar dai wacce take cikin jin ciwo a lokacin da take yi mata wanka. Sai ta tambayeta mai ya sameta, sai ta gaya mata abinda ya faru.

Mrs Ekenta ta ce ta samu mijin nata tayi masa magana akan abinda yasa yayi lalata da ‘yar tashi, ya amsa laifinsa, amma yace da hannun yayi amfani ba gabansa ba. Bayan kai ta asibiti, an gano cewa da gabanshi yayi amfani.

Ta ce ta kai karar wannan abu ga ‘yan uwan mijin nata, amma sai suka yi mata barazanar za su yi mata duka idan ta gayawa wani.

Kwamishinar harkokin mata da yara ta jihar, Ndidi Mezue, ta ce wannan cin zarafi ne mai tsanani, ta ce har yanzu yarinyar tana cikin ciwo.

Kwamishinar ta ce jim kadan bayan samun labarin abinda ya faru, sunyi gaggawar zuwa wajen, inda suka kama shi tare da taimakon jami’an DSS. Ta ce zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here