Alhamdulillah: Mutum 74 da suka kamu da Coronavirus a jihar Kano sun warke

0
140

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa mutum 74 da suka kamu da cutar Coronavirus a jihar sun warke.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ita ce ta sanar da wannan labari mai dadi a daren jiya Talata da misalin karfe 11:50, inda ta ce a ranar kawai an samu karin mutane 27 da aka gano suna da cutar a jihar.

A yanzu haka dai rahotanni sun nuna cewa mutane 693 ne suka kamu da cutar a jihar.

Mutum 83 sun warke daga cutar, inda mutane 33 kuma suka riga mu gidan gaskiya. Inda mutane 586 suke kwance a asibiti suke cigaba da karbar magani a hannun jami’an hukumar lafiya.

A ranar Litinin dinnan ne gwamnatin jihar ta bayyana tsawaita dokar hana zirga-zirga a jihar ta tsawon mako daya.

Haka a rahoton da shafin yanar gizo na gidan rediyon freedom dake Kano ya bayar, ya bayyana cewa a jiya Talata gwamnan jihar ya gana da Sarakunan gargajiya na jihar, inda ya bukaci su mai da hankali wajen wayarwa da al’umma illar wannan cuta ta Coronavirus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here