Alhaji Yusuf Lateef: Malamin da yayi kokarin aurar yarinya ‘yar shekara 16 a matsayin mata ta 9 kotu ta hana

0
245

Mai shari’a Aderemi Adegoroye dake jagorantar wata kotu a Akure, dake jihar Ondo, ya dakatar da Alhaji Yusuf Lateef, daga auren wata yarinya ‘yar shekara 16 a matsayin mata ta 9.

A yadda rahoto ya bayyana, Lateef ya nemi iyayen yarinyar su bashi aurenta a shekarar 2019, a lokacin tana shekara 15. Duk da yarinyar taki amincewa, amma iyayenta suka tilasta ta akan sai ta aure shi, aka saka ranar daurin aure. Yarinyar sai ta gudu daga gidansu a ranar daurin aure, inda dan uwanta ya taimaka mata ta gudu Akure.

An bayyana cewa taje ta kai karar iyayenta wajen ma’aikatar harkoki da cigaban mata ta jihar. Bayan an bata wurin zama sai aka fara nema mata hakkinta wajen dakatar da auren.

An gurfanar da Alhaji Lateef tare iyayen yarinyar a gaban kotu da laifin karya doka ta uku a kundin shari’ar jihar Ondo ta shekarar 2007.

A ranar Juma’a 22 ga watan Mayu, kotu ta yanke hukunci, inda ta bukaci yarinyar ta koma gidan iyayenta, sannan aka sanya Alhaji Lateef ya rubuta takarda kan cewar babu shi babu ita, sannan ya tabbatar da babu wani abu da zai sameta.

Da take magana akan wannan shari’a kwamishinar harkoki da walwalar mata ta jihar, Titilola Adeyemi, ta ce yarinyar ta koma gidan iyayenta inda shi kuma Malamin aka yi masa gargadin fita harkar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here