Akwai takaici idan na tuna matata ce ta mayar da rayuwata haka – Aliyu Umar wanda matarsa ta yankewa azzakari

0
441

Ranar Talata 30 ga watan Yuni, 2020, ita ce ranar da Aliyu Umaru ba zai taba mantawa ba a rayuwar shi. Ita ce ranar da matarsa Halima, ta sanya wuka ta yanke masa azzakari.

Ya sha bakar azaba a lokacin da yake kwance a Asibitin Koyarwa na Tarayya dake jihar Gombe, inda aka kwantar da shi bayan faruwar lamarin a jihar Taraba.

Umaru ya ce: “Ni mai sayar da magungunan dabbobi ne, shekaru 42 ina da mata guda biyu da ‘ya’ya guda biyu.

“Uwargidan tana da namiji, Amaryar kuma tana da mace. Uwargidan Halima tana da ciki. Muna zaune a Tella cikin karamar hukumar Gasso, jihar Taraba. An canja mini asibiti daga Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya dake Taraba zuwa Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake Gombe.”

Umaru dai yayi bayanin, yadda lamarin ya faru cikin takaici, inda ya cigaba da cewa: “Bayan na dawo daga wajen aiki, na samu ruwan zafi nayi wanka, na kuma ci abincin da matata tayi mini kafin na kwanta bacci. Daga baya na tashi cikin wani irin radadin gaske, na kwala ihu.

“Ina dubawa naga matata ta yanke mini azzakari. Daga baya ne aka sanar da makwabta. Ban sani ba ko an saka mini wani abu a cikin abinci ko ruwan da na sha kafin nayi bacci. Matata ta gama da rayuwata.”

Rahotanni sun nuna cewa mijin da amaryar suna samun matsala da Halima tun kafin wannan lamari ya faru.

A cewar kanin wanda lamarin ya faru da shi, Usman mai shekaru 40, ya ce akwai yiwuwar hakan na da nasaba da abinda mahaifiyarsu ta umarce su da su bar garin inda ita kuma Halima ba ta so hakan ba.

Usman ya ce: “Mu ‘yan asalin garin Lukari ne, muka dawo Tella saboda matsala. Sun kama gida, suna shirin dawowa daga Tella zuwa Jalingo a ranar Lahadi.

“Da tsakar dare ne kawai naji waya ta tana kara, sai na daga, naji dan uwana yana gaya mini abinda ya faru. Cikin gaggawa aka kai shi asibiti a Taraba don tsayar da zubar jinin. Amma sun ce basu iya wannan aiki ba saboda basu da kayan aiki. Daga nan ne suka ce mu samu inda yafi mu kai shi.

Ya ce dan uwanshi yana kokari wajen yiwa matan nashi adalci.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here