Akwai sauran tsalle: Gwamnatin tarayya ta sake shawara kan bude makarantu

0
473

Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu ba ta bayar da damar bude makarantu ba a fadin Najeriya.

Shugaban kwamitin gudanarwa na yaki da cutar COVID-19, kuma sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, shine ya bayyana haka a jiya Alhamis 2 ga watan Yuli, yayin da yake bayani game da komawa makarantun, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Da yake magana a wajen taron kwamitin a Abuja, shugaban ya ce iya daliban da za su yi jarrabawa kawai za a bari su koma makaranta domin maimaita karatun da suka yi a baya kafin jarrabawar.

“Saboda gujewa shakku, ba za a bude makarantu ba. Iya daliban da suke bukatar rubuta jarrabawa kawai za a bari su koma su maimaita darasin da suka yi a baya kafin jarrabawar,” ya ce.

“Kamar yadda muka sanar daku, ma’aikatar ilimi ta kasa za ta yi shawara da masu ruwa da tsaki domin bayar da ka’idoji na komawa makaranta baki daya.

Ya bukaci iyaye da su tabbatar da ‘ya’yansu suna amfani da fasahar zamani ta karatu a yanar gizo da aka kawo.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here